Milkshake na kankana abin sha ne mai daɗi, musamman a lokacin zafi. Yana haɗa zaƙin kankana da laushin madara, wanda ke sa ya zama abin sha mai ƙoshin lafiya da sauƙin yi a gida. Milkshake na kankana yana ƙara kuzari, musamman a lokacin zafi. Haɗuwar zaƙin kankana da madara yana ba da ɗanɗano mai dadi da kuma taimakawa wajen rage ƙishin ruwa. Milkshake na kankana yana da sauƙin hadawa a gida ba tare da wani wahala ba ko tsadar kayan haɗi ba, wanda hakan ya sa kowa zai iya yin sa cikin sauƙi a kowani lokaci.
Abubuwan hadawa
- Kankana
- Madaran ruwan gwangwani daya
- Sukari yadda ake bukata
- Ka saka kankara domin ya yi sanyi Idan kina so
Yadda ake hadawa
Abi wadannan matakai masu sauki dan hada milkshake na kankana mai dadi.
- Ki samu kankanarki mai kyau, ki bare
- Ki cire ƙwayoyin kankanan sannan ki yanka shi ƙanana.
- Kiyi blending a blender dinki irin su vitamix immersion blender.
- Idan kina so ki tace ko kuma ki barshi haka da dan tsaki tsakin kankanar.
- Sai ki zuba madararki da sukari yadda ki ke bukata.
- Sai ki kuma blending yadda za su hade jikinsu.
- A sa a firji ko a sha a haka kamar yadda za’a iya shan lemun virgin chapman.
Shi kenan milkshake na kankana ya kamala.





