Ku koyi yadda ake lemun mangoro da abarba cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi hude ne da steps uku kacal.
Abubuwan hadawa
- Mangoro
- Abarba
- Sugar
- Ruwa
Yadda ake hadawa
- Ki samo mangoro da abarba ki bare ki yanka su kanana.
- Sai ki dauko blender ki zuba su a ciki, ki sa sugar da ruwa ki nika su.
- In sun niku sai ki tace ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha ko ki sa kankara sai a sha.