Skip to content

Yadda ake jollof rice mai kwai

Share |
Yadda ake jollof rice mai kwai
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

A yau za mu koyar da yadda ake jollof rice mai kwai. Kafin nan mai karatu na iya duba girkinmu na baya inda muka koyar da yadda ake coconut jollof rice . To mai karatu ga yadda ake jollaf rice mai kwai daki daki:

Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshe shinkafa
  2. Dafaffafen nama (ki yanka kanana)
  3. Kwai
  4. Man gyada
  5. Cucumber (ki yanka kanana)
  6. Kayan kamshi
  7. Tarugu (ki jajjaga)
  8. Maggi
  9. Albasa (ki yanka)
  10. Ganyen ugu (ki yanka)
  11. Lawashi (ki yanka)
  12. Kabeji
  13. Tumatur

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki dauko kabeji, tumatur da albasa ki yanka su kanana ki wanke da vineger (za ki zuba ruwan vineger kadan a ciki ruwan wankewar) ko ki sa gishiri kadan sai ki wanke ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
  2. Dauko kwan ki fasa a kwano sai ki dauko albasa da gishiri kadan ki sa ki juya. Sai ki daura non stick pan akan wuta kidan diga butter ko man gyada idan ya danyi zafi sai ki zuba kwan a ciki ki rufe nadan wani lokaci sai ki juya ki juya (sai ki yi scrambling) idan ya yi sai ki ajiye a gefe.
  3. Daura tukunya akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama shima, sannan ki dauko yankakken namanki ki sa a ciki ki juya nadan seconds
  4. Zuba ruwan dumi (dai dai wanda zai karasa dafa miki shinkafanki) sai ki zuba kayan kamshi, gishiri kadan da maggi,(iya dandano da zai mi ki) ki rufe nadan wani lokaci. 
  5. Da zarar kinga ya fara tafasowa sai ki kawo tafasashshe shinkafa ki zuba a ciki ki juya har sai komai ya bi jikin shinkafan, sai ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye (shinkafanki ya nuna) sai ki kawo ganyen ugu, lawashi, cucumber da kwanki (wanda Kika scrambling abaya) ki zuba, ki juya shinkafan ya hade da su ganyen da kwan, sai ki rufe tukunya ki na kamar minti 2 (amma ki rage wuta sosai).
  6. Sai ki sauke ki sa a plate ki zuba kabejin ki da Tumatur akai kamar yanda ki ka gani a hoto. A ci dadi lafiya.

Za a iya duba girkinmu na baya kamar yadda ake jollof rice da dankalin turawa da yadda ake native jollof rice da makamantansu duk a cikin Bakandamiya. 

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×