Lemun kankana da abarba na daya daga cikin lemuka ko in ce juice masu saukin hadawa ga kuma rashin yawan kayan hadi, uwa uba kuma ga dinbin amfani. Ku biyo mu domin ganin yadda ake wannan lemu.
Abubuwan hadawa
- Kankana
- Sugar
- Abarba
- Ruwa
Yadda ake hadawa
- Za ki yayyanka kankana ki nika ki tace ki sa sugar ki sa a fridge
- Abarba shima za ki yayyanka ki niqa ki tace ki sa sugar ki sa a fridge.
- Sai sunyi sanyi kalau sai ki ciro ki dauko kofin da za ki sa a ciki ki fara zuba na abarban kafin ki zuba na kankana a samansa, a ashafa dadiy lafiya!
za ku iya duba girke-girkenmu na baya, kamar, yadda ake gashin kifi karfasa da sauransu. Kar ku manta da za ku iya binciko duk wani kala abinci da kuke so a nan Bakandamiya Kitchen.