Barkan mu da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya Kitchen. Muna maku fatan alkhairi a wannan sabuwar shekara. A yau na zo muku da recipe na yadda za a hada watermelon milkshake a saukake. Ga shi kamar haka:
Abubuwan hadawa
- Kankana (1)
 - Sugar
 - Ice cream (strawberry flavour)
 - Madara (2 cups)
 
Yadda ake hadawa
- Farko za ki yanka kankana ki barta tare da yayan cikin ta domin suna da matukar amfani ga lafiya.
 - Ki sa kankana a blender ki sa ice cream ki sa milk dinki a ciki sai ki markada. Za ki markada shi ne sosai har sai yayi smooth.
 - Ki zube a bowl ki sa sugar sai ki saka shi a fridge ko a saka kankara a sha.
Mai karatu wannan shine yadda ake watermelon milkshake. Sannan za a iya duba girke girkenmu na baya. 

