Skip to content

Yadda ake hada vegetable rice

Share |
yadda ake hada vegetable rice
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Yau zan gabatar mana da yadda ake hada vegetable rice.

Abubuwan hadawa

  1. Peas
  2. Green beans
  3. Carrots
  4. Inibi
  5. Basmati rice/Ko normal shinkafa dangote

Yadda ake hadawa

  1. Farko idan basmati rice za ki yi amfani da ita to za ki jiqa ta ne na tsawon awa 1 kafin amfani idan kuma normal rice ce shikenan Ki yanka Veggies dinki strips (dogaye) ko ki yi su in cubes.
  2. Ki dora ruwa a tukunya idan sun tafasa sai ki zuba shinkafa ki matsa lemun tsami ciki ki rufe.
  3. Bayan mintina idan ta fara dahuwa sai ki bude ki zuba veggies dinki ki rufe.
  4. Idan ta dahu da sauran ruwan za ki zuba ta a colander ta tsane shikenan sai ki mayar a tukunya ta dan tsane ki saka inibi (raisin). Kin gama ke nan. Za a iya ci da miya daban daban, kamar potatoe soup, cabbage sauce, onion sauce da sauran su.
    Mai karatu zai iya duba girke-girke da dama a wannan dandali na Bakandamiya Kitchen.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×