Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya Kitchen. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalun da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada ugwu-egusi soup.
Abubuwan hadawa
- Ugwu leaf
- Egusi
- Tarugu da tattasai (t&t)
- Albasa
- Seasoning
- Manja
- Garlic
- Beef/Kifi
- Kwai
Yadda ake hadawa
- Farko za ki saka manja a pot sai ki sa albasa ki juya ki zuba grated t&t dinki a ciki ki motsa.
- Ki saka garlic a ciki ki yanka albasa mai dan yawa ki zuba. Ki wanke ugwu leaf ki yanka shi sai ki saka, Ki yayyafa yan ruwa ba da yawa ba.
- Ki sa seasonings da maggi idan ganyen ya fara dahuwa sai ki hada egusi. Ki zuba egusi a bowl ki fasa kwai ki kwaba shi da kauri. Ki dinga diban wannan paste ki na sawa kaman yadda ake saka kosai. Ki rufe na yan mintina sai ki bude ki juya, idan ya dahu sai a ci da ko wane irin tuwo.