Ku koyi yadda ake hada sweet pancakes cikin sauki. Wannan pancake na bukatan abubuwan hadi tara ne da kuma steps uku kacal.
Abubuwan hadawa
- Filawa
- Sugar
- Baking powder
- Kwai
- Chocolates
- Nutella
- Dark chocolates
- Maltesers
- Smarties
Yadda ake hadawa
- Farko kaman na spicy pancake shima za ki zuba flour a cikin bowl ki dama da ruwa. Sai ki fasa kwai ki sa whisk ki sake hadawa a saka baking powder da pinch na salt.
- Ki dora non-stick pan akan wuta, ki yi brushing da mai. Ki zuba batter ki rufe sai ya yi. Haka za ki ta yi har ki gama.
- Ki jera su, idan kin dora daya ki sa Nutella a tsakiya sai kin gama ki zuba melted chocolate a sama. Ki zuba sauran chocolate a kai. A yanka a ci.