Skip to content

Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

Share |
yadda ake hada spinach soup
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake hada spinach soup (miyan masa) mai dadi ga kuma kyau. Wannan miyar masa gangariya ne dan gargajiya mai dauke da salon zamani.

Abubuwan hadawa

  1. Manja
  2. Albasa da lawashi
  3. Kayan miya
  4. Naman rago
  5. Allayaho
  6. Maggi
  7. Tafarnuwa
  8. Mixed spices

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki tafasa nama ki yanka albasa a cikin tafashen ki sa maggi, idan ya yi ki zube da ruwan a gefe sai ki mayar da tukunyar.
  2. Ki zuba manja a cikin tukunyar sai ki saka albasa idan ya fara soyuwa sai ki zuba kayan miya da ki ka nika. Ki rufe ki ba shi yan mintina dan su soyu, idan ki ka juya sai ki zube wannan ruwan tafashen da naman a ciki.
  3. Ki zuba su maggi da tafarnuwa ki rufe. Sai ki yanka allayaho dinki,ki sheka ma shi ruwan zafi akai (amfanin yin hakan dan colour din ya fito yadda yake) Ki zuba allayaho dinki ki juya idan ta dahu sai a sauke. A ci lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×