Ga yadda ake shortbread cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi biyar ne da steps shida kacal.
Abubuwan hadawa
- Flour 2 cups
- Milk 1 cup
- Sugar 1 cup
- Butter 1
- Baking powder 1 tspn
Yadda ake hadawa
- Farko za ki zuba butter da sugar a cikin mixing bowl. Ki yi mixing dinsu har sai sun hade jikinsu sosai.
- Sai ki saka madara da flour ki zuba baking powder.
- Ki saka hannunki sai ki murza flour har ta hade.
- A saka wannan hadin a fridge na tsawon mintina 5 sai a fito da shi a yi rolling a sa cookie cutters a fitar da shapes.
- Idan ki ka gama sai ki gasa a cikin oven na tsawon 15 minutes.
- Sai a fitar da shi ki saka Nutella a tsakiya ki rufe da wani dayan. A ci lafiya
Muna godiya so sai allah ya kara basira 👏