Skip to content

Yadda ake hada savoury stuffed yam balls

Yadda ake hada savoury stuffed yam balls
0
(0)

Mu koyi yadda ake hada savoury stuffed yam balls cikin sauki. Kayan hadi guda bakwai sannan matakan hadawa guda shida kacal.

Abubuwan hadawa

  1. Doya
  2. Tarugu
  3. Nama (ground beef)
  4. Seasoning
  5. Breadcrumbs/flour
  6. Kwai 2
  7. Albasa da lawashi

Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki fere doya ne sai ki dafa ta har ta dahu. Ki cire ta ki tsane ruwanta sannan sai ayi mashing dinta ko a dan daka ta a turmi.
  2. Ki saka tarugu, da lawashi da albasa a ciki.
  3. Ki cire yolk na kwai ki sa shi a ciki ki ajiye whites din a gefe.
  4. Ki saka salt da seasoning na ki sai ki hade shi sosai ko ina ya ji.
  5. Sai ki dinga sawa a tafin hannunki ki sa stuffing na naman ki ko kaza ko ma kifi. Ki rufe shi kaman ball.
  6. Sai Ki dora mai a wuta ki sa salt ki kada egg white dinki. Za ki sa balls din a cikin Breadcrumbs sai ki tsoma a cikin ruwan kwai ki sake sawa a breadcrumbs sai cikin mai a soya. Idan baki da breadcrumbs za ki iya amfani da filawa. A ci lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×