Skip to content

Yadda ake hada savoury cake

Share |
Yadda ake hada savoury cake
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Uwargida ki shirya tsaf dan ganin yadda ake hada savoury cake.

Abubuwan hadawa

  1. Flour
  2. Baking powder
  3. Parsley
  4. Maggi
  5. Man gyada
  6. Tarugu
  7. Albasa
  8. Lawashi
  9. Dankali
  10. Cabbage
  11. Carrots
  12. Kwai

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba filawa ki dama ta da ruwa ki fasa kwai ki zuba a ciki. Sai ki saka parsley, da tarugu, da lawashi a ciki. Ki ajiye butter din  a gefe don ki hada filling na ki.
  2. Za ki fere dankali ki yanka kanana, da carrots. Ki soya dankalin sama sama. Sai ki kwashe ki zuba yankakken koren tattasai, da carrots a ciki da maggi.
  3. Idan ya dahu ki na juyawa sai ki saka cabbage ki juya ki sauke. Ki dora nonstick pan a kan wuta ki zuba batter dinnan ya bi jikin pan gaba daya. Idan ya yi ki juya ki cire. Haka za ki ta yi da butter din har sai kin gama.
  4. Ki shimfida ko wane daya ki saka filling ki nade shi kaman nadin tabarma. A saka ketchup a sama domin garnishing.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×