Skip to content

Yadda ake hada prawn chutney

Share |
yadda ake hada prawn chutney
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake hada prawn chutney ga dadi ga kuma kyau. Wannan hadin prawn din na da saukin gaske wajen yi.

Abubuwan hadawa

  1. Prawn
  2. Albasa
  3. Spices
  4. Man gyada
  5. Curry leave
  6. Tafarnuwa
  7. Tumatur 5 (a markada)
  8. Maggi seasoning

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki wanke prawns din ki sosai sai ki zuba shi a cikin tukunya ki saka spices da maggi ki dora pan mai dan zurfi akan wuta ki zuba man gyada ki yanka albasa.
  2. Idan ya yi zafi sai ki saka tafarnuwa da curry leave na ki. Sai ki zuba tumatur da tattasai da tarugu da ki ka nika, ki juya.
  3. Idan ya soyu sama sama sai ki zuba cup 1 na ruwa a ciki ki juya sai ki zuba wannan prawns na ki da ki ka yi marinating. Ki dafa sai prawns din ya yi laushi ya dahu. A ci lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×