Ku koyi yadda ake hada potato soup cikin sauki. Wannan recipe na bukatan abubuwan hadi guda bakwai ne da kuma steps hudu don hadawar.
Abubuwan hadawa
- Dankali (irish)
- Tattasai da tarugu
- Seasoning
- Albasa da lawashi
- Veggies (peas, da beans,da karas)
- Anta ko qoda
- Man gyada
Yadda ake hadawa
- Farko za ki zuba mai a pot ki zuba grated tattasai da tarugu da albasa ki juya, sai ki zuba stock (ruwan tafashe) a ciki idan babu ki zuba cup na ruwa daya Sai ki rufe.
- Idan ya tafasa sai ki zuba veggies da ki ka yanka yadda ki ke so. Ki sa seasoning da spices ki sake rufewa.
- Bayan mintina biyu sai ki wanke dankalin, sannan sai ki zuba dankalin da ki ka wanken a ciki (ba za ki yanka dankalin ba).
- Wannan soup ba a so dankalin ya dagargaje dan haka ba za ki bari har ya dafe ba.. Idan ya yi sai a sauke a zuba a shinkafa ko abunda aka girka a ci.