Skip to content

Yadda ake hada porridge with ganache mix

Share |
Yadda ake hada porridge with ganache mix
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake hada porridge with ganache mixi. Wannan recipe ne da za a hada shi da kayan hadi takwas kacal cikin matakai biyar.

Abubuwan hadawa

 1. Kayan ciki
 2. Dankali
 3. Albasa da lawashi
 4. Taugu da tattasai
 5. Maggi da seasoning
 6. Man gyada
 7. Carrots
 8. Peas

Yadda ake hadawa

 1. Na wanke kayan ciki ne sai na dora shi a tukunya na sa albasa da spices na bar shi ya dan fara dahuwa ya rage karfi sosai.
 2. Sai nasa mai a wani tukunya daban, nasa chopped tattasai da attarugu dina. Na kawo kayan cikinnan da na tafasa nasa a ciki. Na yanka carrots, sannan na hada green peas nasa.
 3. Bansa ruwa ba sai da suka dauko soyuwa, sai na zuba sauran romon pepper soup na kaza da nake da (left over). Idan ba ki da romon kuma ki sa ruwa.
 4. Na bari ya fara tafasa sannan na zuba dankalin da na rigaya na gyara shi na raba shi bibbiyu. Dama ruwan pepper soup din bai da yawa dai-dai abinda zai dafa dankalin ne. Dankali nan da nan yake dahuwa.
 5. Da naga ya yi sai na yanka cucumber mai yawa na sa. Ruwan bai tsotse ba na sauke na kawo soyayyen nama da nayi pepper meat da shi na zuba a sama na yanka boiled egg, na hada wannan ne da home made tamarind drink. A ci lafiya.

Abun lura

Kada ki ce don pepper soup ya kare za ki bar romon, a’a ki ajiye shi. Yana da amfani!

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading