Uwargida ki biyo ni ki ga yadda a yau zamu hada pineapple ginger mojito.
Abubuwan hadawa
- Abarba
- Cucumber
- Ginger
- Sugar
- Flavour
- Sprite
Yadda ake hadawa
- Farko uwargida za ta gyara ginger, ta cire bayan, sannan ta yanka ta kanana.
- Sai ki yanka cucumber da abarba Ki zuba su baki daya cikin blender.
- Ki zuba Sprite ki yi blending.
- Idan ya yi ki tace shi ki saka kankara. Ki sa sugar. Sannan, ki saka flavor. A sha lafiya.
Za ku iya duba sauran girke-girkenmu da kalolin drinks da muka koyar a baya, kamar: Yadda ake hada natural feminine juice da sauransu.