A yau kuma zan koya mana yadda ake hada pepper soup na kassa/kasusuwa. Harwa yau mai karatu zai iya duba daruruwan makalunmu da muka gabatar a baya a kan girke-girke.
Abubuwan hadawa
- Tarugu da tattasai (T&t)
- Kassa/kasusuwa na rago ko sa
- Maggi and seasoning
- Albasa da lawashi
- Tafarnuwa
- Ginger
Yadda ake hadawa
Ki wanke kassa ki sa a cikin pot ki zuba ruwa ya fara dahuwa. Idan ya rage karfi ya soma dahuwa kenan sai ki zuba wayancan kayan hadin da muka lisafo baki daya ki yi ta dafa shi sai ya yi zai dauki kaman awa daya da rabi dan ya dahu sosai. A ci lafiya.
Za a iya duba: Yadda ake hada miyar edikainkong da yadda ake hada net crepes da sauransu.
Photo Credit: Anita Abiona