Skip to content

Yadda ake hada net crepes

Yadda ake hada net crepes
0
(0)

Ku koyi yadda ake hada net crepes. Wannan crepes ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Fulawa
  2. Baking powder
  3. Food colour (na yi amfani da green da yello)
  4. Kwai (1)
  5. Gishiri
  6. Gorar ruwa (empty)
  7. Meat filling/cabbage filling/potato filling (kaman yadda muka yi bayanin hadin naman samosa ko meat pie) 

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba fulawa da baking powder, kwai da gishiri a bowl ki yi mixing sai ya yi smooth sosai kuma ba da kauri ba.
  2. Sai ki raba shi, ki sa duk colors da ki ke so.
  3. Ki samu gora ki huda marfin kaman huduwa hudu.
  4. Ki zuba batter a cikinshi. Ki dora non-stick pan akan wuta ki shafa mai.
  5. Ki dinga zuba batter na cikin gorannan ta koina a wannan pan din, ya yi saka-saka.
  6. Idan ya yi ki cire ki sa wani. Idan kin gama duka ki cire. Ki zuba filling a ciki ki rufe. Ki rufe kamar rufin shawarma. A ci lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×