Ku koyi yadda ake hada net crepes. Wannan crepes ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Fulawa
- Baking powder
- Food colour (na yi amfani da green da yello)
- Kwai (1)
- Gishiri
- Gorar ruwa (empty)
- Meat filling/cabbage filling/potato filling (kaman yadda muka yi bayanin hadin naman samosa ko meat pie)
Yadda ake hadawa
- Farko za ki zuba fulawa da baking powder, kwai da gishiri a bowl ki yi mixing sai ya yi smooth sosai kuma ba da kauri ba.
- Sai ki raba shi, ki sa duk colors da ki ke so.
- Ki samu gora ki huda marfin kaman huduwa hudu.
- Ki zuba batter a cikinshi. Ki dora non-stick pan akan wuta ki shafa mai.
- Ki dinga zuba batter na cikin gorannan ta koina a wannan pan din, ya yi saka-saka.
- Idan ya yi ki cire ki sa wani. Idan kin gama duka ki cire. Ki zuba filling a ciki ki rufe. Ki rufe kamar rufin shawarma. A ci lafiya.