Ga yadda ake hada natural zobo drink, mu koya ‘yanuwa. Wannan zobo ne mai dadi da sauki hadawa waddan za a iya baiwa duk kowa da kowa
Abubuwan hadawa
- Zobo
 - Sugar
 - Abarba
 - Lemu
 - Foster clerks
 - Berries (tiara)
 - Flavour (Vanilla ko strawberry)
 
Yadda ake hadawa
- Farko za ki zuba sobo a cikin tukunya ki sa mi shi ruwa. Sai ki fere abarba ki sa bawonta a cikin dahuwar sobon ki nika abarba ki tace ruwanta ki ajiye a gefe.
 - Sauran tukar ki sake maida su a cikin ruwan dahuwar sobo. Za ki dafa sobon nan na ki har ya tafasa. Sai ki tace shi ki sa awani wuri.
 - Ki kawo ruwan abarba da ki ka nika ki zuba su a ciki ki sa sugar a ciki sai ki sake zubawa a pot ki mayar ya yi ta dahuwa kaman mintina 10.
 - A sauke yadan sha iska sai ki sa flavour da foster clerk dinki a ciki. A sa kankara a sha, ko a sa shi a fridge.
 

