A yau zamu koyar da yadda ake hada natural feminine juice. Uwargida wannan juice na da saukin hadawa ga kuma amfani. Ki gwada ki bamu labari!
Abubuwan hadawa
- Lemun tsami
- Cucumber
- Mango
- Kankana
- Abarba
- Lemun zaki
- Sugar
Yadda ake hadawa
- Farko za ki wanke duk wa’yannan fruits da muka lissafo a sama.
- Ki yanka ki gyara ki cire bayan.
- Ki saka su a blender ki nika sosai.
- Ki kara ruwa sai ki tace. Ki saka sugar kadan. Ki sa kankara ko a saka shi a fridge ya yi sanyi. A sha lafiya.