Skip to content

Yadda ake hada miyar kuka

miyar kuka
0
(0)

Miyar Kuka na ɗaya daga cikin shahararrun miya a ƙasar Hausa, musamman a arewacin Najeriya da wasu sassan Afirka ta Yamma. Ana yin wannan miya ne da garin ganyen kuka (ganyen itacen baobab da aka busar aka niƙa), wanda ke ba ta ɗanɗano na musamman da kuma kauri.

Miyar Kuka tana da sauƙin hadawa, kuma ana iya yin ta da kayan haɗi kamar nama, kifi, ko bushashshen kifi. Haka kuma ana amfani da kayan ƙamshi kamar albasa, kanunfari, barkono, da kayan miya domin ƙara mata armashi.

Yawanci ana cin Miyan Kuka tare da abinci irin su tuwon dawa, tuwon masara, ko tuwon shinkafa. Miyar tana da muhimmanci a al’adun Hausawa, domin tana daga cikin abincin gargajiya da ake yawan amfani da shi a gidaje da bukukuwa.

A taƙaice, Miyan Kuka ba abinci ne kawai ba, har ila yau tana nuna al’ada da tsarin rayuwar Hausawa.

Abubuwan hadawa

  • Garin kuka
  • Nama ko kaza
  • Attarugu da tattasai
  • Daddawa
  • Manja
  • Maggi da gishiri
  • Kayan kamshi
  • Albasa

 Yadda ake hadawa

Abi wadannan matakai masu sauki don samun miyar kuka mai dadin gaske.

  1. Ki daka daddawa ki hada da citta da masoro idan ta daku sai ki zuba attarugunki da tattasai.
  2. Ki ci gaba da dakawa har sai sunyi laushi.
  3. Daga nan kuma sai ki kwashe ki ajiye a gefe ki wanke albasarki ki yankata.
  4. Ki dora tukunyarki a wuta ki zuba manja ki soya idan ya soyu sai ki wanke namanki ki zuba a cikin manjan.
  5. Ki saka maggi da gishiri ki rufe.
  6. Za kiga yana soyuwa kuma yana dahuwa, daga nan sai ki zuba jajjagenki da ki kayi ki rufe zuwa minti biyar.
  7. Sai ki zuba ruwan miyarki ki kara maggi da gishiri ki zuba albasa sai ki rufe ki barta tayi ta tafasa.
  8. Da ga nan sai ki kada ta ki dinga zuba kukarki a hankali, kina burgawa har tayi kaurin da kike bukata.
  9. Sai ki kuma rufeta zuwa minti biyar sai ki sauke. Skinenan miyar kukan ki ta hadu.Za ki iya cin ta da tuwon dawa, tuwon shinkafa ko tuwon alkama, har ma da farar shinkafa kamar yadda ake yi a Maiduguri.
  10. Za ki iya hada ta da sanyayyar lemun abarba mai dai gaske.

Za a iya duba yadda wasu miyoyin kamar miyar kori da kuma miyar karkashi da sauransu.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×