Ku koyi yadda ake lemun abarba mai dadi ga kuma kyau. Wannan lemun abarba na da saukin gaske wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Abarba
- Ruwan sanyi
- Sugar
- Mint leaf
- Danyar citta
- Ruwan lemun tsami
Yadda ake hadawa
- Ki bare abarba ki yanka ta kanana ki sa a blender, ki sa ruwan sanyi, sugar, ginger ki rufe ki yi blending sai ki tace.
- Ki samu serving glass ki dan daka mint leaf, ki zuba pineapple juice da ruwan lemun tsami kadan ki juya. A sha lafia.
Karin bayani
Ba lallai sai da ruwam sanyi za ki yi ba za ki iya amfani da kankara ko kuma bayan kin tace ki sa a fridge ya yi sanyi.
In ba ki da mint leaf za ki iyayin sa haka, haka shima lemun tsami ba lallai ba ne.