A yau kuma zamu duba yadda ake hada miyar kubewa (Okro Soup) da Kifi.
Abubuwan hadawa
- Danyen kubewa
- Tattasai
- Tarugu
- Albasa da lawashi
- Maggi da seasoning
- Busashen kifi
- Danyen kifi
- Garlic
- Ginger
- Manja
Yadda ake hadawa
- Farko za ki yi grating na kubewa ki aje ki yi grating na tattasai da tarugunki aje gefe.
- Ki dora manja a wuta ki yanka albasa a ciki. Ki sa grated tattasai da tarugu a ciki ki juya sai ki sa kifin ki danye ki rufe yadan sulala kadan.
- Ki bude ki sa ruwa kamar kofi 3 ko kuma dai dai iya ruwan miyar da ki ke so.
- Idan ya tafasa sai ki saka seasoning dasu garlic da busashen kifi da ki ka gyara.
- Ki rufe, bayan yan mintina sai ki bude Ki zuba kubewan dinki da kanwa. Kar ki rufe haka za ki dafa shi idan ya yi ki sauke Aci lafiya.Amfanin kanwa anan yana kara mata yauqi
Wannan shine yadda na ke miyar kubewa. Mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya kamar: spinach soup (miyar masa), da sauransu.
Photo Credit: MyActiveKitchen