Ku koyi yadda ake hada milky nut pap. Wannan recipe ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Farar shinkafa ta tuwo
- Gyada
- Madara
- Dabino
- Sugar
Yadda ake hadawa
- Farko za ki jika farar shinkafa sai ki gyara gyada ki cire mata duk bawon bayan. Ki hada ta da shinkafa da dabino a nika sosai.
- Sai ki zuba ruwa ki tace shi. Wannan taceccen ruwan (kullun) da ki ka samu su zaki dora akan wuta ki na juyawa a hankali, amma kar a cika wuta.
- Za ki ga yana kara fari yana kauri. Idan ya yi dai dai sai ki sauke a zuba madara da sugar ko a bari sai idan za a sha.
Wannan kunun yana da dadi sosai ga karin lafiya. A sha lafiya.