Meatballs (ƙwallon nama) wani irin abinci ne da ake yi daga nama niƙaƙƙe wanda ake gaurayawa ko cakudawa da kayan haɗi da kayan ƙamshi kaman su kwai, tafarnuwa, attarugu da sauran kayan kamshi da dandano. Ana dunƙule naman ya zama ƙananan ƙwallaye, sannan a soya ko a dafa su. Abinci ne mai daɗi kuma ana iya ci da shinkafa, taliya ko burodi.
Meatballs yana da sauƙin hadawa kuma yana da amfani ga jiki saboda yana ɗauke da sinadaran gina jiki kamar su protein. Akwai meatballs kala-kala ko nau’o’i kala kala wanda zamu lissafo kamar haka;
- Meatballs na naman sa (Beef meatballs)– Ana yin su da naman sa. Su ne mafi shahara kuma suna da ɗanɗano mai ƙarfi.
- Meatballs na naman kaza (Chicken meatballs)– Ana yin su da naman kaza. Sun fi sauƙin narkewa kuma suna da laushi.
- Meatballs na naman akuya (Goat meatballs)– Ana yin su da naman akuya, suna da ɗanɗano na musamman kuma ana yawan amfani da su a wasu al’adu.
- Meatballs na kifi (Fish meatballs)– Ana yin su da kifi maimakon nama. Sun dace ga masu son abinci mai sauƙi ko masu guje wa jan nama.
- Meatballs na kayan lambu (Vegetable meatballs)– Ana yin su da kayan lambu kamar wake, dankali, ko karas. Sun dace ga masu cin ganyayyaki (vegetarians).
- Meatballs da cuku (Cheese-stuffed meatballs)– Ana saka cuku a ciki domin ƙara ɗanɗano da laushi.
- Meatballs mai miya (Meatballs with sauce)– Ana dafa su tare da miya kamar ta tumatir ko gravy domin su zama masu laushi da ɗanɗano mai yawa.
Abubuwan hadawa
- Nikakken nama
- Albasa
- Attarugu
- Kwai
- Tafarnuwa
- Garin busashen Burodi
- Mai
Yadda ake hadawa
Meatballs na da saukin hadawa idan aka bi wadannan matakai masu sauki.
- Da farko uwargida zata hada nikakken naman ta da albasa. Zaki iya nika naman ki cikin AAOBASI meat grinder.
- Sai ki yanka attarugu kanana kanana ko ki jajjaga, ki sa maggi da gishiri da kuma nikakken tafarnuwa a cakuda sosai.
- Sai ki fasa kwai a ciki ki kara cakudawa. Bayan nan sai ki rinka diban naman da cokali irin ta ice cream scooper ta kitchen Aid ko da hannu, sannan ki cura ko kiyi shaping dinsa kamar kwallo.
- ki saka a ruwan kwai sannan ki barbade shi da garin busashshen burodi.
- Idan soyawa zaki yi sai ki zuba su a cikin manki da kika daura mai zafi ki soya.
- Idan ya nuna zaki ga yayi golden brown kuma yayi crispy ta wajen sa.
- Zaki ya amfani dasi cikin jollof na shinkafa, a cikin stew, cikin vegetable spaghetti ko ma ki ci meatballs din hakan nan.
Aci dadi lafiya!






