Ku koyi yadda ake hada ginger bread ga dadi ga kuma kyau. Wannan ginger bread na da saukin gaske wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Flour 1.3 cups
- Mixed spice 2 tablespoon
- Nikaken ginger 3 teaspoon
- Man gyada
- Sugar 1½ cup
- Golden syrup 1 cup
- Kwai 3
- Ruwan dumi 1 cup
- Bicarb 2 teaspoon
Yadda ake hadawa
- Farko za ki tankade fulawa dinki ki saka nikaken ginger da mixed spice a ciki sai ki hada kwai, da sugar da man gyadan ki a wuri daya a cikin wani bowl daban ki hada da syrup ki juya
- A hankali sai ki dinga zuwa flour da ki ka tankade a cikin wannan hadin na cikin bowl har ya hade sai ki saka baking soda da ruwa kadan dan dough dinki ya hade jikinsa.
- Ki saka a cikin tray gasa ko pan din gasa biredi ko pan din cake ki gasa shi na mintina 25 @ 180 degree.
What does the chef mean by 1.3 cup of flour
1.3 cup means 1 cup and 0.3 cup. If you’re to divide 1 cup of flour into 10 then 0.3 would be 3 out of that 10.