Skip to content

Yadda ake hada crispy samosa

Share |
Yadda ake hada crispy samosa
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake crispy samosa mai dadi. Wannan samosa ce da idan kun gwada ba za ku sake komawa baya ba. Sai an gwada…

Abubuwan hadawa

Fillings

  1. Tsokar nama/mince meat
  2. Tarugu
  3. Albasa da lawashi
  4. Maggi
  5. Gishiri
  6. Carrots
  7. Green pepper

Batter

  1. Corn Flour
  2. Fulawa
  3. Egg (1)
  4. Salt

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki dora namanki a pot ya dahu sosai ki sa seasoning. Sai ki zuba shi a turmi ki daka ko ki yi mincing, sannan ki saka albasa, da carrots da ki ka yanka kanana da su tarugu, sai ki juya ki dan ba shi tsoro na minti biyu ki sauke.
  2. Bari mu hada batter. Za ki samu bowl ki zuba flour da corn flour kadan ki sa ruwa ki dama sosai kar ya yi kauri kuma kar ya yi ruwa.
  3. Ki fasa egg ki saka sai gishiri da maggi kadan. Za ki dora pan non-stick ki na shafo wannan batter da brush ki na brushing pan din, kafin ki gama shafawa ma za ki ga da kanshi ya taso.
  4. Sai ki cire ki aje ki sake yi. Idan kin gama sai ki yanka wannan wrap gida 4 ki na saka filling ki na nadewa kaman triangle.. Sai ki soya su a man gyada da ya yi zafi idan ya yi brown sai a kwashe.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×