Ku koyi yadda ake hada buttered chicken mai dadi ga kuma kyau. Wannan miyar buttered chicken saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.
Abubuwan hadawa
- Kaza
- Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)
- Albasa
- Yoghurt
- Butter
- Fresh cream
- Gishiri
- Yaji
- Butter
Yadda ake hadawa
- Farko za ki yanka kazan dai dai yadda ki ke so. Ki samu bowl ki zuba ta a ciki ki zuba yoghurt da garlic and ginger da gishiri da albasa da ya ji ki shafe jikin kazar ko ina ya ji sosai.
- Ki rufe ki bar shi tsawon mintina 5 sai ki dora frying Pan akan wuta Ki zuba butter a ciki sai ki zuba kazar nan ta ki za ki dafa ta on low heat har na tsawon 35 minutes.
- Idan kinga ruwan na tsotsewa sai ki saka yoghurt ko fresh cream ko wane za ki iya sakawa. Idan ta yi sai a sauke za ki iya dafa wannan miyan aci da sakwara ko semo amala ko yadda duk ki ke so. A ci lafiya.