Ku koyi yadda ake hada butter-shaped cookies ga dadi ga kuma kyau. Wannan hadin cookies din na da saukin gaske wajen yi.
Abubuwan hadawa
- Flour 2 cups
 - Sugar 1 cup
 - Butter 250grm
 - Baking powder 1tspn
 - Kwai 1
 - Icing sugar
 - Egg white
 
Yadda ake hadawa
- Farko za ki mixing sugar da butter na tsawon mintina 3, idan suka hade sannan ki fasa kwai ki saka.
 - Ki hade su sannan ki sa flour da baking powder a cikin hadin.
 - Ki ci gaba da mixing har sai ya yi smooth. Ki zuba wannan hadin cikin piping bag sai ki dinga piping dor flower akan tray kaman yadda suke a jikin picture.
 - Idan ki ka gama sai a gasa. Za ki iya barin shi haka ko ki yi icing kamar haka:
 
Za ki fasa eggwhite ki hada da icing sugar idan suka yi kauri ki dinga saka gefe daya ko duka cookie a ciki sai ki cire shi ki saka cikin sprinkles.

