Skip to content

Yadda ake hada bread cheese balls

Yadda ake hada bread cheese balls
3.3
(3)

Ku koyi yadda ake hada bread cheese balls cikin sauki. Makatai shida kacal uwargida za ta bi domin hada wannan girki.

Abubuwan hadawa

  1. Dankalin turawa (Wanda aka dafa akayi mashing)
  2. Yaji
  3. Maggi
  4. Flour
  5. Corn flour
  6. Corn flakes (nikakke)
  7. Bread slices
  8. Cheese
  9. Man gyada

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki samo bowl ki zuba dankalin da aka dafa akayi mashing na shi ki saka, sai ki saka yaji, da maggi da sauran spices da ki ke so, ki saka bread slices ki ci gaba da juyawa da hannunki har sai biredin ya shige ciki baki daya.
  2. Sai ki samo wani bowl daban ki saka flour kadan da corn flour ki dama su da ruwa
  3. Ki saka corn flakes dinki a cikin plate ki ajiye shi gefe shima.
  4. Sai ki dinga diban wannan hadin na dankali kina flattening dinshi a hannunki sai ki saka cheese ki mulmula ya zama ball, haka za ki yi su har ki gama baki daya.
  5. Sai ki dinga tsoma balls din cikin ruwan flour sai ki yi coating da cornflakes sai a soya.
  6. Idan ya yi golden brown sai a juya a cire.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×