A yau zamu duba yadda ake hada bitter leaf soup, miya ce mai dadi a baki,ga magani, ba sai na tuna muku amfanin shuwaka wurin gyara ciki ba.
Abubuwan hadawa
- Manja
- Nama
- Seasoning
- Garlic
- Ginger
- Shuwaka (bitter leaf)
- Tattasai
- Tarugu
- Albasa
Yadda ake hadawa
- Farko za ki yanka nama ki sa ruwa a ciki ki yanka albasa ki dora shi akan wuta.
- Sai ki yanka shuwaka dinki itama ki zuba ta a cikin tukunya ki tafasa ta (amfanin wannan zai cire maki dacin shuwaka har yara su iya cin ta su ma).
- Sai ki zuba wannan shuwaka a cikin blender ki yanka albasa mai yawa ki nika su a tare, ki aje gefe dan ci gaba da hada miyarki.
- Ki zuba nikakken tattasai da tarugu a cikin ruwan naman ki dake tafasa sai ki juya, ki saka manja ki rufe.
- Bayan mintina biyu sai ki sake budewa ki juya ki saka seasoning da garlic and ginger na ki a ciki, Ki dauko nikakken shuwaka da albasa da ki ka hada ki zuba a ciki ki juya.
- Ki rufe ya dahu, sannan ki dandana ko da bukatar karin gishiri a miyar ki. Za ki iya cin wannan miyar da ko wane irin tuwo. Aci lafiya.
Zaku iya duba wasu miyoyinmu da muka yi a baya, kamar su Miyar hanta, miyar sure (yakuwa) da sauransu.