Ku karanta yadda ake ground beef sauce cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi goma da kuma steps uku kacal.
Abubuwan hadawa
- Nama (na yi amfani dana gwangwani)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Tumatur (ki yanka)
- Tattasai (ki yanka)
- Kayan kamshi
- Maggi
- Gishiri
- Karan albasa (ki yanka)
- Mai ko butter
- Lawashi (ki yanka)
Yadda ake hadawa
- Idan bakida naman gwangwani za ki iya amfani da nama mai kyau marar kitse. Da farko ki sami namanki mai kyau ki gyara ki wanki ki daura kan wuta ya dahu sai ki sauke ki sami turmi ki daka shi ya daku sosai sai ki kwashe, ajiye a gefe.
- Daura tukunya akan wuta ki sa butter ko man gyada ki yanka albasa ki kawo namanki ki zuba sai kina juyawa a hankali, sannan ki kawo tarugu, da tattasai ki sa, da albasa sai ki juya shi a hankali, sannan ki kawo kayan kamshi, da maggi (iya dandanon da zai mi ki) ki sa, sai ki kawo tumatur ki sa ki juya (za ki iya dan kara ruwa kamar cokali 3) sai ki rage wuta ki rufe tukunyarki nadan wani lokaci.
- Daga karshe sai ki kawo ganyen lawashi ki sa a ciki ki juya sai ki sauke. Ita wannan sauce ana cinta da shinkafa, Taliya, macaroni da dai sauransu. A ci dadi lafiya.