Skip to content

Dahuwar farar shinkafa

Dahuwar farar shinkafa
0
(0)

Yau ga yadda ake dahuwar farar shinkafa mun kawo muku. Ga shi nan dai girki ne da kamar a rufe ido a yi shi to amma shima yana bukatar natsuwa domin ya yi kyau a sami yadda ake so.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa kofi (gwargwadon yadda ake so)
  2. Gishiri
  3. Ruwa

Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki dora ruwanki a wuta ya tafasa.idan ya tafasa sai ki kawo shinkafarki ki zuba ki dan motsa kisa gishiri sannan ki barshi kamar minti uku.
  2. Sai ki tace ki wanke shinkafarki ki tsaneta.
  3. Sai ki dora tukunyarki a wuta ki sa ruwa dan daidai misali sai ki rufe kibar shi minti ashirin idan yayi sai ki sauke ki kwashe zaki ganta wara-wara ta yi kyau.

Za’a iya ci da miyar dage-dage. A ci dadi lafiya. Na gode.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×