Uwargida ga yadda ake fish egg sauce cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi sha biyu da kuma steps biyar.
Abubuwa hadawa
- Kifi dafaffe (ki bare sala sala ki cire kaya)
- Kwai dafaffafe (ki yanka)
- Tarugu (ki yanka)
- Butter
- Man gyada kadan
- Tumatir (ki yanka)
- Koren tattasai (ki yanka)
- Ruwan silalenki kifi.
- Albasa
- Maggi
- Kayan kamshi
- Gishiri kadan
Yadda ake hadawa
- Daura tukunya ki akan wuta ki sa butter ki kawo man gyada kadan ki sa sai ki yanka albasa a ciki ki soya sama sama.
- Sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama sannan ki kawo ruwan silalenki kifi ki ki sa a ciki ki juya.
- Dauko kayan kamshi, maggi iya dandano da zai miki ki zuba a ciki ki juya da gishiri kadan ki sa ki juya.
- Sai ki dauko tumatir ki sa ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
- Daga nan sai ki kawo dafaffafen kifin ki ki sa ki juya a hankali sai ki kawo dafaffafen kwanki ki sa ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan. Daga nan sai ki sauke.
Ana iya cin wannan sauce da alala, taliya, shinka ko macaroni da dai sauransu. A ci dadi lafiya.