Skip to content

Yadda ake faten wake da dankali

Share |
Yadda ake faten wake da dankali
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake faten wake da dankali cikin matakai biyar masu sauki.

Abubuwan hadawa

 1. Wake (dafaffe)
 2. Dankalin turawa (dafaffafe)
 3. Jajjagen Tarugu da albasa (grated)
 4. Ganyen albasa (lawashi)
 5. Manja(mai kyau)
 6. Albasa
 7. Maggi(9ja pot)
 8. Kyan gamshi (Spices)
 9. Crayfish (in ana bukata)
 10. Gishiri

Yadda ake hadawa

 1. Ki sa tukunyanki akan wuta ki sa manja, sai ki kawo albasarki ki yanka a ciki ki soya sama sama.
 2. Sai ki dauko grated tarugu da albasa ki sa a ciki ki juya.
 3. Sai ki kawo spices naki ki sa a ciki da su maggi da crayfish ki sa sai ki juya, anan sai ki kawo ruwan zafi kadan (idan a kwai ragowar ruwan dahuwar wakenki) ki sa ki rufe tukunya ki har sai Kinji Ya fara tafasa.
 4. Daga nan sai ki dauko wakenki tare da dankali ki sa a ciki ki juya a hankali ki rufe tukunyanki nadan wani lokaci.
 5. Daga karshe sai ki kawo ganyen albasarki ki sa a ciki, ki rufe tukunyanki na dan wani lokaci, sai ki sauke. A ci dadi lafiya

Sai mun hadu a girki na gaba.

Rate the recipe.

Average: 4 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading