Skip to content

Yadda ake fanke mai madara da kwai

Share |
Yadda ake fanke mai madara da kwai
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ga yadda ake fanke mai madara da kwai cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi bakwai ne da steps uku kacal.

Abubuwa hadawa

  1. Filawa kofi biyu
  2. Yeast cokali daya
  3. Gishiri kadan
  4. Sugar rabin kofi
  5. Kwai biyu
  6. Madarar gari cokali uku
  7. Ruwan dumi

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu kwano ko roba ki sa filawa, yeast, madarar gari, gishiri kadan, sugar, kwai, ki juya su sai ki sa ruwan dumi ki dama shi kada ki dama da ruwa ruwa kuma kada ya yi kauri sosai.
  2. Ki buga shi sosai sai ki rufe da murfin kwanon kibar shi na sawon minti talatin ya taso.
  3. Bayan ya tashi sai ki ciro ki daura mai akan wuta, in ya yi zafi sai ki na sawa kina soyawa.

Karin bayani

  1. Tashin panken ki zai danganta ne da kyaun yeast naki, idan bashida kyau sosai zaifi minti talatin kamin ya tashi.
  2. Kada ki cika mata wuta in ki ka cika zai kone.
  3. A duk lokacin da za ki yi amfani da wani abu wadda yake bukatar yeast toh ki yi amfani da yeast mai kyau in ba hakaba ba zai tashi ba.
  4. Idan ki ka yi amfani da ruwan dumi kwabin ki zai fi tashi da wuri.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake fanke mai madara da kwai”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×