Skip to content

Yadda ake egg muffin

Yadda ake egg muffin
3
(1)

Ku karanta yadda ake egg muffin daki-daki ta hanya mai sauki.

Abubuwan hadawa

  1. Kwai Dafaffafen
  2. Dankali turawa(ki yanka Kanana)
  3. Dafaffafen nama (saiki yanka shi Kanana Kanana)
  4. Koren tattasai (yankakke)
  5. Tarugu (yakkake)
  6. Albasa (itama ki yanka)
  7. Maggi
  8. Curry da thyme
  9. Gishiri kadan
  10. Butter Ko man miya (vegetable oil)
  11. Baking power

Yanda ake hadawa

  1. Ki hada yankakkun kayan ki; namanki, albasa, tarugu dasu dafaffafen Kwan ki da sauransu. Amma kar ki sa dafaffafen dankali
  2. Ki kawo Curry da thyme kadan ki sa, Ki dauko Maggi na ruwa kisa (za ki iya amfani da su ne normal Maggi). Sai ki juya ki ajiye a gefe
  3. Ki sami karamin kwano ki fasa kwanki a ciki sai ki sa baking powder (? tsp kadan dan da Kwai 3 za kiyi amfani ). Sai gishiri kadan Saiki kara juyashi .
  4. Sai ki dauko muffin pan naki ki Shafa mishi veg oil ko butter sai ki dauko step zuwa step 3 a ciki 6 sai, ki dauko kwanki ki sa akai.
  5. Sannan ki dauko Dafaffafen dankali (yankakke) kisa a ciki .
  6. Sai ki sa egg muffins naki a preheated oven ki gasa har sai ya gasu (ya zama golden brown).
  7. Za ki iyaa ci haka ko kuma ki hadashi da soyayyen dankali turawa.. Aci dadi lafiya

Sai mun hadu a girki na gaba.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×