Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya Kitchen. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada dambun shinkafa mai gyada.
Abubuwan hadawa
- Gyada
- Shinkafa (wadda aka gyara aka barza)
- Seasoning
- Zogale
- Albasa da lawashi
Yadda ake hadawa
- Farko za ki hade zogale da shinkafa da gyada ki yayyafa masu ruwa ki zube ya turara bayan mintina 10 sai ki sauke.
- Ki zube shi cikin bowl babba ki sa chopped tattasai, da tarugu, da albasa, da seasoning da man gyada da sauran kayan hadi.
- Anan za ki sake mayar da wannan hadin a cikin tukunyar da ki ka dora marfi ciki ya sake turara sosai. A sauke a ci lafiya.
I really learn alots thru your cooking
Inshallah