Ga yadda ake couscous ta yi wara-wara, mu koya ‘yanuwa. Sannin yadda za a dafa couscous ta yi wara-wara na da muhimmanci, uwargida.
Abubuwan hadawa
- Couscous
- Man gyada ko butter
- Tomato
- Koren tattasai
- Kwakwamba (Cucumber)
- Albasa
Yadda ake hadawa
- Da farko ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwa ki rufe na dan wani lokaci
- ki dauko couscous na ki ki zuba shi a cikin kwano sai ki dauko man gyada ko butter ki zuba a ciki sai ki juya har sai man gyadan ya game jikinsa duka.
- Idan ruwa ya tafasa sai ki juye couscous naki a ciki sannanki rage wuta (Karki cika ruwa sosai)
- Dauko tumatir, albasa, koren tattasai da cucumber ki wanke ki gyara ki yanka su kanana sai ki sake wankewa da gishiri ki tsane su (kar kibar ruwa a jiki).
- Idan couscous naki yayi sai ki juye a wani abu(kwano babba) sai ki diba su tumatur da kwakwamba da ki ka yanka ki sa a ciki sai ki juya ki sa a a faranti.
Ana ci da Ko wacce irin miya (kamar miyar taushe, miyar stew da sauransu).
A ci dadi lafiya.