Ku koyi yadda ake crunchy Nigerian meat pie mai dadi ga kuma kyau. Meat pie din na da kyau zai bada cruncy pie mai ban saha’awa idan aka yi.
Abubuwan hadawa
- Flour 500g
- Magirine (simas) 250g
- Egg one
- Baking powder 2 teaspoon
- Salt pinch
- Nutmeg 1teaspoon
Fillings
- Nama 1/2kilo
- Dankalin turawa 250g
- Attaruhu
- Albasa
- Sinadarin dandano da sauran kayan kanshi wato spices
- Carrots
- Oil (man gyada) 1tablespoon
Yadda ake hadawa
- Da farko za ki fara hada fillings dinki ki sa man gyadanki cokali daya a tukunyarki mai tsafta ki wanke namanki ki markada shi tun yana danye.
- Sai ki sa shi a tukunya idan ya fara turara sai ki sa kayan kamshinki da sinadarin dandano ki cigaba da juyawa. Bayan yan mintuna zaki ga ya canza kala daga kalanshi na danyen nama. Sai ki kawo ruwanki dan daidai kar ya shanye kan naman na ki ki zuba.
- Ki wanke carrots dinki da Irish potato dinki ki yayyankasu sai ki zuba a cikin tukunyan namanki ki dan kara ruwa ki rufe tukunyarki ya dahu na yan mintuna.
- Sai ki samun flour cokali daya ki dama shi da ruwa kadan bayan namanki ya sake dahuwa sai ki zuba filling da kika dama ki sake rufe shi na wasu mintuna .saiki sauke shi ki ajiye a gefe yayi sanyi.saiki koma kan hada dough dinki
Yadda ake kwaba dough din meat pie
- Idan da so samu ne da flour da magirine dinki kisa su a fridge yayi sanyi kafin kizo kwabawa. Gurin kwabin ma kiyi amfani da ruwa fridge dalili shine samun abunda muke cewa crunchy pies.
- Ki samu kwanonki mai tsafta ki auna flour dinki kan scale idan baki da scale kiyi amfani da measuring cups. Idan zakiyi amfani da measuring cup zaki auna cup hudu na flour mai sanyi, sannan ki kawo baking powder ki zuba, ki zuba gishiri pinch. Sai ki kawo butter dinki mai sanyi shima ki matseshi a cikin flour ki murza shi. Za ki ga yana murmushewa.
- Sai ki kawo ruwan kankararki. ki zuba kadan kada kina hade shi, baya bukatan kwabi da yawa hada shi za ki ringa yi.
- Idan ya hadu sai ki samu leda mai tsafta ki sa shi a cikin fridge ki barshi na dan mintuna, bayan ya huta sai ki daukoshi ki samu rolling pin da board ki yanka shi dan daidai daidai.
- Sai ki murza idan kina da cutter sai kiyi amfani dashi idan kuma baki da cutter ki samu cup ki fitar da circular shape sai ki rufe da fork.
- Idan kina da oven za ki preheating din oven dinki idan ya dau zafi ki jera su a baking tray ki sa ki fasa kwanki ki shafa ma dough dinki ki sa shi ki gasa na 40 minutes.
- Idan baki da oven zaki samu foil paper ki lullube pan dinki sai ki samu gishiri mai dan yawa ki zuba a aluminium pot ki sa a wuta ya dau zafi kisa dough dinki ki rufe
A ci dadi lafiya.
The recipe is well articulated.
I love it.
Wow!
Allah ya bada sa’a sister👌👏
Looking nice and welldone.
Tnx alot, more recipes are coming inshallah
Very nice
Allah y bada da sa a Ina sanshi sosai
It’s delicious, I love it.
it’s delicious, I like it
Ina so na ki ya ne
Okay,kiyi min magana a WhatsApp 09075792991, nagode
Masha Allah