Skip to content

Yadda ake coconut and watermelon smoothie

Share |
Yadda ake coconut and watermelon smoothie
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake coconut and watermelon smoothie cikin sauki, abubuwan hadawa guda hudu, matakai guda biyar da kuma karin dabaran inganta shi.

Abubuwan hadawa 

  1. Kankana
  2. Kwakwa
  3. Yoghurt
  4. Madara (peak milk)

Yadda ake hadawa

  1. Ki cire bakin jikin kwakwanki (ya zama fari tas), sai ki goge a jikin abun goge kubewa (grater).
  2. Sai ki sa a blender ki sa ruwa (amma ruwan bawai mai yawa ba) sannan ki markada har sai kin ga ya yi laushi.
  3. Sai ki cire ki tace ruwan ki zubar da dusan, anan sai ki ajiye ruwan kwakwan a gefe.
  4. Ki dauko kankana ki gyara shi ki cire bakaken kwallayen da ke ciki, ki yanka kanana ajiye a gefe.
  5. Dauko blender ki sa kankananki tare da ruwan kwakwa, sannan ki fasa madara ta peak (ko kuma idan baki da peak za ki iya sa cokali hudu ko fiye na madarar gari a wani kofi daban sai ki zuba ruwan sanyi sosai, iya ruwan da kika sa iya gardinsa). Sannan ki markada har sai kinga ya yi laushi sun markadu sosai, sai ki sa a kofi ki sa kankara Ko kuma ki sa a fridge ya kara sanyi. A sha dadi lafiya.

Karin bayani

Idan ki navso za ki iya tacewa yazama iya ruwan kankana dana kwakwa za ki sha ba tare da tikar kankana ba.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading