Skip to content

Yadda ake chocolate cake

Share |
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Na tabbata uwargida kina cikin masoya cake, plain ne, mai topping ne, cream ne, to ga su nan dai kala kala. A yau dai yadda ake chocolate cake ne zamu koyar. Uwargida dau biro da takarda, bismillah.

Abubuwan hadawa

  1. Sugar kofi 1
  2. Filawa kofi 2
  3. Cocoa Powder kofi 1
  4. Kwai 10
  5. Butter (Sima’s) 1
  6. Baking powder  1/2 tsp
  7. Flavour 1/2 tsp
  8. Brown chocolate color (1 tblspn)

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki hada butter da sugar ki buga su sosai da muciya ko Mixer.
  2. Ki fasa kwai daya bayan daya kinasawa kina hadawa.
  3. Idan kin ga sun hade sai ki sa flour, da cocoa powder, da baking powder, da flavour dinki da brown chocolate color.
  4. A zuba a farantin gasa cake, a yi pre heating na oven a gasa na tsawon mintina 45.
  5. Idan ya yi a cire a yanka slices kaman yadda muka sa a jikin hoto. Za ki iya topping na chocolate da nutella chocolate ko hubby Ko vanoise chocolate. Za ki sa shi a leda ne sai ki dinga zubawa jikin cake din.

Wannan shine yadda na ke chocolate cake. Na gode, mai karatu na iya duba girkinmu na baya, kamar: Yadda ake hadin doughnuts da sauransu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×