Ga yadda ake chocolate buns masoya girkin Bakandamiya Kitchen. Ku biyo mu ga yadda ake yi dalla dalla.
Abubuwan hadawa
- Filawa kofi 2
- Baking powder cokali karami 2 (tspn)
- Butter cokali babba 2 (tbsp)
- Sugar cokali babba 3
- Gishiri kadan
- Madara ¼ kofi
- Nutmeg ½ cokali
- Ruwa ½ kofi
- Chocolate (irin na kanana ma leda yan naira 40-50)
Yadda ake hadawa
- Ki tankade filawarki a kwano mai dan girma, sai ki zuba baking powder, nutmeg, madarar gari, gishiri sai ki juya.
- Dauko butter ki sa a cikin filawa ki murja har sai ya hade jikansa sai ki sa sugar, ki fasa kwanki a ciki da ruwa ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki ajiye a gefe na dan wani lokacin kamar minti 15-20.
- Daura man gyada akan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko chocolate na ki ki na sawa a kwabin filawa kina kamar mulmula shi kina soyawa a mai har sai ya soyu (karki cika masa wuta don kar ya miki tuwo a ciki) sai ki tsane a matsani. A ci dadi lafiya.
Mai karatu wannan shine yadda ake chocolate buns. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba. Amma kafin nan, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: yadda ake egg roll shawarma da kuma yadda ake potato balls da makamantansu.