Skip to content

Yadda ake Chinese rice

Share |
yadda ake Chinese rice

Ku koyi yadda ake Chinese rice ta hanyar bin steps masu sauki.

Abubuwan hadawa

 1. Dafaffafiyar shinkafa (wanda aka dafa da gishiri)
 2. Karas (carrots)
 3. Peas (na gwangwani)
 4. Albasa
 5. Kwai
 6. Tattasai
 7. Butter
 8. Gishiri

Yadda ake hadawa

 1. Da farko za ki fasa kwanki a ciki wani karamin kwano sai ki yanka mishi albasa, sai ki sa gishiri kadan sannan ki ajiye a gefe.
 2. Ki yanka su tattasai, albasa kanana, sai ki yanka karas na ki (ki sa masa tafasashshe ruwan zafi da baking powder ki rufe nadan wani lokaci sannan ki tace).
 3. Ki bude peas naki na gwangwani ki juye shi a kwano sai ki zuba mishi ruwa sosai sannan ki tace. Anan sai ki hada duk veggies naki dukka wuri daya ki ajiye a gefe.
 4. Ki daura non stick pan naki akan wuta ki sa butter ki a ciki idan ya narke sai ki kawo kwanki ki sa a ciki, sai ki rika juyawa, (kamar yadda ake miyar kwai)
 5. Idan yayi sai ki dauko su carrot da ki ka gyara ki ka ajiye su wuri daya sai ki zuba a ciki ki juya a hankali dan karya kama.
 6. Sai ki dauko dafaffafiyar shinkafa ki sa a ciki ki juya a hankali har sai ya yi.
 7. Sai ki sauke ki sa a plate ki kawo miyar stew ki sa.
Add to Lists (0)
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page