Skip to content

Yadda ake chicken potato salad

yadda ake chicken potato salad
4.5
(2)

Chicken potato salad, hadin salad ne da ya wadatu da ingantattun kayan lambu, yana da dadi sosai musamman idan kika hada shi da fried rice ko jollof rice ko ma ki ci shi da bread, hmm! karshen dadi kenan, ku biyo mu dan ganin yadda ake hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Tsokar Kaza
  2. Mixed Spices
  3. Kayan Dandano
  4. Dafaffen Dankali
  5. Dafaffen Kwai
  6. Dafaffen Karas
  7. Green Pepper
  8. Celery

Yadda ake hadawa

  1. Ki dau tsokar kaza ki sa masa kayan dandano da kayan kamshi ki cakude. Ki gasa shi a kan frying pan , sai ki yayyanka kanana.
  2. Ki yayyanka dankali da karas da green pepper da persley duka kanana.
  3. Sai ki hade su duka wuri guda ki cakude kisa mixed spices dandano da kuma mayonnaise. Shikenan sai ki yi serving chicken potato salad dinki.

Wannan recipe an koyar da shine a Ramadan Recipes 2025 Webinar wanda Chef Shaima Alhussainy ta gabatar.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×