Chicken potato salad, hadin salad ne da ya wadatu da ingantattun kayan lambu, yana da dadi sosai musamman idan kika hada shi da fried rice ko jollof rice ko ma ki ci shi da bread, hmm! karshen dadi kenan, ku biyo mu dan ganin yadda ake hadawa.
Abubuwan hadawa
- Tsokar Kaza
- Mixed Spices
- Kayan Dandano
- Dafaffen Dankali
- Dafaffen Kwai
- Dafaffen Karas
- Green Pepper
- Celery
Yadda ake hadawa
- Ki dau tsokar kaza ki sa masa kayan dandano da kayan kamshi ki cakude. Ki gasa shi a kan frying pan , sai ki yayyanka kanana.
- Ki yayyanka dankali da karas da green pepper da persley duka kanana.
- Sai ki hade su duka wuri guda ki cakude kisa mixed spices dandano da kuma mayonnaise. Shikenan sai ki yi serving chicken potato salad dinki.
Wannan recipe an koyar da shine a Ramadan Recipes 2025 Webinar wanda Chef Shaima Alhussainy ta gabatar.