Ku koyi yadda ake tuwon shinkafa da miyar agushi. Wannan hadin shinkafa da miyar agushi yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Shinkafa na tuwo (gwargwadon yadda ake bukata)
- Agushi
- Tattasai 3
- Attarugu 3
- Albasa 1
- Nama 1/2
- Kifi 3
- Maggi 6
- Mai
- Tafarnuwa 3
- Gishiri
- Ledan kulla shinkafar
Yadda ake dafa tuwon shinkafar
- Da farko zaki dora ruwanki awuta
- Sai ki wanke shinkafarki ki tsaneta sosai kidan baza tasha iska
- Idan ruwan ya tafasa sai ki kawo shinkafarki ki zuba ki dan motsa da muciya saiki rufe kibashi minti ashirin
- Idan yayi sai ki tukeshi ki kawo leda kina kullawa
Yadda ake dafa miyar agushi
- Da farko zaki wanke namanki kisa albasa da maggi ki dora a wuta
- Idan ya yi sai ki kwashe ki zuba mai da kayan miyanki da ki ka markada sai ki rufe
- Idan ya dan soyu sai ki zuba ruwan tafasashen nama kisa maggi, da gishiri, da nama, da tafarnuwa, da agushi sai ki rufe ya samu kamar minti biyar
- Idan yayi zaki ji yana kamshi sai a sauke a ci da tuwon shinkafa
Very nice