Tuwon madara kayan kwalama ne mai matukar dadi, wanda mutane suna son shi, sai dai wasu yana ba su gardama a wurin yi. Ku biyo ni domin ganin yadda nake yin nawa.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups milk (lactorich)
2- 1/2 cup sugar
3- 1/2 cup water
Yadda ake yi:
1- ki zuba sugar da ruwa a cikin pan dinki mai kyau irin na Bakandamiya shopping.

2- Sai ki rage wuta ki bari suga ya gama narkewa ya dan fara danko.

3- Sai ki zuba madararki

4- Ki kashe wutar ki yi ta juyawa har sai duka ya hade.

5- Ki juye a kan buhu Ko parchment paper. Sai ki yu flatening dinsa daidai girman da kike so.

6- Ki samu cutter mai kyau ki fitar da shape. Ko mould idan kina da shi. Za kuma ki iya amfani da wuka ki yanka daidai girman da kike so

7- Ga shi nan yadda ya yi kyau.

8- Sai ki packaging yadda kike so
