Stick meat ko in ce tsire, wani nau’in nama ne wanda ake sokawa a jikin tsinken tsire ko skewers na karfe ko kuma na icce. Akan yi shi ne da kuli-kuli ko kuma yaji. A yau na zo maku ne da yanda ake yin tsiren yaji na naman rago.
Abubuwan bukata:
1- 1kg tsokar rago
2- 1 tablespoon mixed spices
3- 1 tablespoon maggi powder
4- pinch of salt
5- 4 tablespoons vegetable oil
6- 3 tablespoons dakakken yaji
7- 1 teaspoon parsley flakes
Yadda ake yi:
1- ki yanka nama da fadi, sai ki zuba seasoning and spices da mai ki motsa sosai yadda za su shiga ciki.

2- a karamin bowl ki zuba mai da yaji da parsley flakes ki motsa su.

3- ki samu skewers dinki ki jera naman a jiki.

4- ki arranging a kan oven tray sannan ki shafe shi da wannan hadin da kika yi na yaji. Daga nan sai ki dauka ki saka a oven ki gasa shi da wutar sama da kasa na awa daya ko kuma sadda kika tabbatar ya gasu

5- Daga nan sai ki ciro ki serving. Ni dai na yi serving nawa da garau garau

akwai kyawawan plates da wasu nau’ukan na kayan kitchen a Bakandamiya shopping.
